Isa ga babban shafi

Kotun Kolin India ta tabbatar da hukuncin soke damar cin gashin kai ga yankin Kashmir

Kotun kolin India ta tabbatar da hukuncin da wata kotu ta yanke a 2019 na soke damar cin gashin kai karkashin dokokin duniya da aka baiwa jihohin Kashmir da Jammu tare da bada damar a gudanar da zaben ranar 30 ga watan Satumbar badi a yankunan.

Yankin Kashmir mai cike da tsaunuka ya dade yana fuskantar tashin hankali
Yankin Kashmir mai cike da tsaunuka ya dade yana fuskantar tashin hankali © Reuters/Danish Siddiqui (File photo/2019)
Talla

Yankunan da ke da rinjayen musulmi na zama guraren da aka shafe shekaru fiye da 75 ana rikici game da mallakar su a tsakanin kasashen Pakistan da India tun bayan samuwar ‘yancin kasan kasashen a 1947.

Hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta yanke a yau, ya biyo bayan kararrakin bukatar hakan da kungiyoyi suka shigar suna bukatar ta tabbatar da hukuncin da kotun kasa ta zartas a baya.

Matukar aka gudanar da zabe a yankunan kamar yadda kotu ta bayar da umarni, zai zama tamkar cikar burin jam’iyyar BJP ta shugaba Narendra Modi, la’akari da yadda ta dade tana gwagwarmayar ganin hakan ta tabbata.

Sai dai Masu kalubalantar wannan mataki na ganin cewa majalisar wakilan Jammu da Kashmir ce kadai za ta iya yanke shawara kan matsayi na musamman na yankin mai cike da tsaunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.