Isa ga babban shafi

Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami da zai iya karade Japan

Korea ta Arewa ta yi gwajin harba makamai mai linzami mai cin dogon zango, wanda zai isa  isa kowane  lungu na kasar Japan da wasu sassan Amurka, a cewar Korea ta Kudu da Japan.

Wannan ne karo na 5 da Korea taa Arewa ta yi gwajin makami mai linzami a wannan shekarar.
Wannan ne karo na 5 da Korea taa Arewa ta yi gwajin makami mai linzami a wannan shekarar. via REUTERS - KCNA
Talla

Wannan ne karo na biyu a cikin ‘yan sa’o’i da Korea ta Arewa ta harba makami mai Linzami bayan da a  daren Lahadi ta yi gwajin wani makami mai linzami da ke cin matsakaicin zango, bayan da ta  caccaki abin da ta kira take-taken yaki da Amurka ke yi.

 

Makamin zai iya yin tafiyar kilomita dubu 15, kuma abin da hakan ke nufi shi ne yana iya kai wa ko ina a kasar Japan da wasu sassan Amurka, kamar yadda mataimakin ministan tsaron Japan, Shingo Miyake ya bayyana.

Korea ta Kudu ta ce makamin da makwafciyarta ta harba mai cin dogon zango ne, wanda ke tafiya daga nahiya zuwa  nahiya, tana mai zarginta da kawo rudani, ta wajen yin biris da kashedin kasashen duniya da kuma kwamitin Tsaro na Majlisar Dinkin Duniya.

Wannan shi en gwajin makami mai Linzami na biyar da Korea ta Arewa ta yi, baya-bayan nan shi ne a watan Yuli, Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami da ke cin dogon zango, lokacin da ta harba makami mai linzami samfurin Hwasong-18.

A watan da ya gabata, Korea ta Arewa ta bada sanarwa cewa ta samu nasarar kaddamar da tauraron dana dam leken asirin soji na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.