Girka-Libya
Girka zata tura talllafin abinci ga ‘yan tawayen Libya
A yau juma’a ne gwamnatin kasar Girka ta bada sanarwar aikawa da jirgin ruwa mai dauke tallafin abinci da magani ga ‘yan tawayen Libya a Benghazi.Jirgin ruwan mai dauke da tallafin zai tashi ne a tsibirin Salamis dake kusa da Athens, kuma ana sa ran zai isa Benghazi cikin sa’o’I 40. Wannan dai wani yunkuri ne karfafawa ‘yan tawayen kwarin gwiwar kifar da gwamnatin Ghaddafi.A watan Aprilu ne kasar Girka ta rufe ofisoshin jekadancinta dake Tripoli a kasar Libya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: