Isa ga babban shafi
EU-Amurka-MDD

Kasashen duniya sun bukaci MDD daukar mataki akan Syria

Kasashen Turai da Amurka da Kasashen Larabawa sun nemi kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kada kuri’ar la’antar zubar da jinin da ake yi a kasar Syria, inda Majalisar ta bayyana cewa sama da mutane 5,000 aka kashe a zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar Al Assad.

Daruruwan masu Zanga-zanga a birnin Homs na syria
Daruruwan masu Zanga-zanga a birnin Homs na syria Reuters
Talla

An bayyana cewa, kasashen Birtaniya da Faransa, da Jamus da Amurka ne zasu jagoranci matakin tunkarar Majalisar Dinkin Duniya.

Jakadiyar Amurka a kwamitin Sulhun, Susan Rice, ta bukaci sauran kasashen duniya domin bada goyan bayansu wajen haramta sayarwa Syria da makamai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.