Isa ga babban shafi
Columbia

Gwamnatin Columbia tace zata katse tattaunawa da ‘Yan Tawaye

Shugaban Colombia Juan Manuel Santos yace zai katse tattaunawa da ‘yan tawayen FARC har sai sun dakatar da yakin sunkurun da suke yi. Wannan na zuwa ne kwanaki, bayan da mayakan suka kai muggan hare haren bama bamai, a kan wasu motoci, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Tutar kasar Columbia
Tutar kasar Columbia
Talla

Sai dai cikin jawabin da ya yi don bukin cikar shi watanni 18 da karbar madafun ikon kasar, shugaba Santos, ya ce akwai yiwuwar hawa teburin sasantawa da mayakan, masu ra’ayin makisanci.

Wani kiyasin da ma’aikatar tsaron Colombia ta gudanar, ya gano cewa kungiyar, da aka kirkiro ta a shekarar 1964, na da mayaka kusan dubu takwas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.