Isa ga babban shafi
Colombiya

Mutane 44 sun Hallaka Sakamakon Zaftarewar kasa a Colombiya

Masu aikin ceto sun ci gaba da samun karin gawarwakin mutanen da suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a kasar Colombiya, inda suka ce akalla mutane 44 suka mutu zuwa yanzu.Sai dai ma’aikatan ceto sun ce sun dan sami tsaiko, sadoda ruwan sama da aka yi a jiya Talata.Yan kasar sun ci gaba da dakon bayanai kan dangin su da kasa ta rufta wa, a daidai lokacin da ake cire tsammanin yuwuwar samun sauran mutane da ran su. Masu hasashen yanayi na ganin za a ci gaba da tafka ruwan sama a kasar har zuwa farkon shekara mai zuwa ta 2012. 

Shugaban Colombiya Juan Manuel Santos
Shugaban Colombiya Juan Manuel Santos © Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.