Canada
An cafke daruruwan masu zanga-zanga a Canada
‘Yan Sandan Canada sun ce sun cafke Dalibai 400 masu zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta a birnin Montreal. An kwashe tsawon watanni Hudu dalibai na zanga-zanga akan karin kudin Jami’ar Quebec.
Wallafawa ranar:
Talla
Daruruwan dalibai ne suka fito a saman titunan Birnin Montreal domin zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta. Sai dai Jami’an tsaro sun ce Zanga-zangar ta saba doka.
Tun a watan Fabrairu ne Dalibai suke gudanar da zanga-zanga bayan gwamnatin Canada ta kara kudaden Jami’ar Quebec da kashi 82.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu