Isa ga babban shafi
Venezuela

Yan adawan Venezuela na gargadin gudanar da zanga zanga akan rantsar da Chavez

Daya daga cikin manyan ‘Yan adawan kasar Venezuela, Julio Borges, ya bukaci gudanar da zanga zanga muddin Gwamnatin kasar ta jinkirta bikin rantsar da shugaban kasa, Hugo Chavez. 

Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez
Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez REUTERS
Talla

Borges ya bukaci al’ummar kasar da suyi shirin shiga zanga zangar, da kuma bijirewa gwamnatin kasar, saboda kaucewa amfani da tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Ya kara da cewar, zasu tafi kungiyoyi da kasashen duniya dan kai karar Gwamnatin kasar su, wadda ke shiri juya kundin tsarin mulkin kasar dan biyan bukatar kanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.