Isa ga babban shafi
Birtaniya

Shugabannin duniya sun mika sakon ta’aziya ga mutuwar Thatcher

Tun da aka ruwaito labarin rasuwar Uwargida Margaret Thatcher a ranar Litinin, Shugabannin kasashen duniya ke ta aiko da sakonnin ta’aziya ga kasar Birtaniya, suna masu jinjina ga irin rawar da Thatcher ta taka a zamaninta. Mikhail Gorbachev da Helmut Kohl da Bill Clinton suna cikin shugabannin da suka aiko da sakon ta’aziyararsu ga iyalan tsohuwar shugabar da suka yi zamani tare.

Margaret Thatcher tsohuwar Firaministar kasar Birtaniya
Margaret Thatcher tsohuwar Firaministar kasar Birtaniya REUTERS/Brian Smith/Files
Talla

Shugabannin kasashen Turai da dama sun aiko da sakon ta’aziyarasu ne tare da tuna Margaret Thatcher da ake kira Iron Lady mai aiki kamar Maza da tarihi ba zai manta da ita ba a karni na 20.

Shugaban Amurka Barack Obama ya aiko da sakonsa yana mai juyayin rashin babbar aminiyar Amurka.

Margaret Thatcher ta mutu ne a ranar Litinin tana da shekaru 87 sakamakon mutuwar jiki.

Tsohon shugaban gwamnatin Jamus Kohl, wanda ya taka rawa wajen hada kan Jamusawa a 1990 yace yana tuna Margaret Thatcher a matsayin shugabar da ke fafutikar tattabar da ‘yanci da gudanar da aiki cikin gaskiya.

Firaministan kasar Australia Julia Gillard tace Thatcher kamar jagora ce da ta bude wa mata kofar shiga a dama da su ga harakokin siyasa a duniya.

Sabuwar shugabar gwamnatin Korea ta Kudu ta dauki Thatcher a matsayin jarumarta tare da jinjina wa tsohuwar shugabar wajen farfado da tattalin arziki Birtaniya a zamanin mulkin ta a 1980.

A sakonsa Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya jinjinawa Margaret Thatcher da cewa ta ci a yaba mata saboda irin rawar da ta taka a tarihin Birtaniya.

Firaministan Faransa Jean-marc Ayrault, cewa ya yi taci kirarin ta na mace mai ran karfe, musamman saboda irin matakan da ta shimfida na tattalin arziki da kyautata rayuwa.

A nashi sakon taaziyyar Shugaban kasar Russia Vladimir Putin yace Thatcher mace ce mai tarin basira.

Ban Ki-moon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jinjinawa marigayiyar musamman a akidarta na siyasa, da hangen nesa musamman yadda ta ja kunnen duniya game da matsalar dimamar yanayi.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Janar Muhammadu Buhari yana daga cikin shugabanin da suka yi mulki tare da marigayiya Margareth Thatcher kuma ya tuna yadda ta karfafa siyasa da tattalin arzikin Birtaniya.

Sai dai a kasar Afrika ta Kudu, shugabannin Jam’iyyar ANC mai mulki sun tuna Thatcher ne a lokacin rikicin wariya a shekarar 1980 tsakani bakaken fata da turawa. A lokacin Thatcher ta fito ta bayyana Jam’iyyar ANC a matsayin kungiyar ‘Yan ta’adda amma duk da haka shugabannin jam’iyyar sun aiko da saon ta’aziyarsu suna masu danganta Thatcher a mastayin shugabar da ba za’a manta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.