Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya za ta sake nazarin bin hanyoyin fitar da Abu Qatada daga kasar

Gwamnatin Birtaniya ta sa ke samun rashin nasara wajen kokarin ganin ta fitar da wani malamin addinin Islama, Abu Qatada daga cikin kasar, inda a karo na biyu, kotun daukaka kara ta ki amincewa da bukatar kasar.Birtaniya na kokarin ganin ta mika malamin ga hukumomin Jordan ne, don fuskantar tuhuma, amma kuma malamin yana cewa idan an mika shi za a ci zarafin sa.Firaministan Britaniya, David Cameron ya sake nuna bacin ransa da hukuncin kotun. yana mai cewa  Abu Qatada, bai kamata ya ci gaba da zama a kasar ta Britaniya ba, domin zaman sa, na da hadari a gare su, za su kuma daukaka kara, kuma za su yi duk abinda ya dace, don fitar da shi daga kasar ta Britaniya. 

Abu qatada
Abu qatada Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.