Putin ya tabbatar da cewa Snowden na birnin Mosco
Shugaban kasar Rasha Vladamir Putin a yau talata ya bayyana cewa Edward Snowden wanda Amurka ke zargi da fallasa bayanan sirri, na cikin birnin Mosco a matsayin wanda ke kan hanyarsa ta wucewa zuwa wata kasa.
Wallafawa ranar:
Shugaba putin wanda ke zantawa da manema labarai ya musanta cewa, kasarsa na da wata yarjejeniya da Amurka dangane da tusa keyar wannan dan taliki zuwa Amurka.
Kafin wadannan kalamai na Putin, kusan ana iya cewa an shiga takun saka tsakanin Amurka da Rasha dangane da batun na Snowden wanda ya shiga kasar ta Rasha a shekaran jiya lahadi amma ba tare da hukumomin kasar sun ce uffan ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu