Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya ce za’a fito fili a bayyana aikin leken asirin Amurka

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sanar da aniyyarsa ta yi wa dokar nan da ke bayar da damar tsananta sanya ido kan ayyukan sadarwa da na asiri a kasar kwaskwarima ba tare da keta hakkin ‘yan kasa ba, wannan kuwa a daidai lokacin da ake ci gaba da yin cece-kuce dangane da fallasa dubban bayanan sirrin kasar da Edward Snowden ya yi.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Jason Reed
Talla

Shugaban Obama wanda ke gabatar da taron manema labarai, ya bayyana cewa duk da ya ke batun tsaro abu ne mai muhimmanci ga Amurka, amma kuma akwai bukatar samar da yarda tsakanin gwamnatin da kuma al’ummar kasar.

Shugaban ya bayyana kudirin gwamnatin shi na fitowa fili a bayyana gaskiyar yadda ake aikin leken asirin Amurka ba tare da wani boyewa ba

Tun a lokacin mulkin tsoho shugaba George W Bush ne dai gwamnati ta yi amfani da hanyoyi daban daban a asirce domin sauraren wayoyi da kuma ayyukan sadarwar al’ummar kasar, a wani abu da gwamnatin ta bayyana shi da cewa matakan yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.