Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar Amurka ta amince da yarjejeniyar kasafin kudin bana

Shugaban Amurka Barack Obama ya jinjinawa ‘yan majalisar dokokin kasar bayan da suka amince da daftarin kasafin kudin kasar a lokacin wani zama da suka gudanar a jiya Talata, wanda hakan ya kawo karshen rashin fahimtar juna tsakanin fadar shugaban da kuma ‘yan majalisa na jam’iyyar Republican.

Shugaban Amurka Barak Obama
Shugaban Amurka Barak Obama REUTERS
Talla

Yarjejeniyar da aka cim ma a Majalisar dokokin, za ta bai wa gwamnatin Obama damar kashe kudade ba tare da wani kangi ba har na tsawon shekaru biyu masu zuwa.

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne dai aka shiga rudani tare da dakatar da ayyukan gwamnatin Amurka saboda rashin kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.