Isa ga babban shafi
Amurka

Za’a janye tallafin da ake ba masu zaman kashe wando a Amurka

Majalisar kasar Amurka ta ki amincewa da matakin tsawaita shirin tallafin da ake ba wadanda ba su da aikin yi a kasar bayan da wa’adin shirin ya kawo karshe a ranar Assabar. Wannan matakin zai shafi Miliyoyan mutanen kasar da ke zaman kashe wando.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS
Talla

Tsohon shugaban kasa ne George W Bush ya kafa gidauniyar tallafawa masu zaman kashe wandon a 2008 inda suke karbar karamin albashi duk wata.

Wannan shirin kuma ya taimakawa miliyoyan Amurkawa fita daga kangin talauci amma ‘Yan Jam’iyyar Republican da ke adawa da gwamnatin Obama sun ce kudaden da aka ware sun yi yawa.

Yanzu haka kuma shugaba Barack Obama yace zai yi kokari wajen ganin majalisa ta amince a tsawaita shirin idan ‘Yan majalisun sun dawo hutu a farkon watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.