Isa ga babban shafi
India-Amurka

India da Amurka suna takun saka

Dangantar Diflomasiya tsakanin Amurka da India ta shiga wani yanayi inda Gwamnatin India ta kaddamar da wani mataki da mayar wa da Amurka da martani bayan cafke wata babbar jami’ar diflomasiyarta a birnin New York.

Wata kungiyar mabiya Rashtrawadi Shiv Sena da ke zanga-zangar kin jinin Amurka bayan cafke wata Babbar Jami'ar Diflomasiyar kasar a New York
Wata kungiyar mabiya Rashtrawadi Shiv Sena da ke zanga-zangar kin jinin Amurka bayan cafke wata Babbar Jami'ar Diflomasiyar kasar a New York REUTERS/Ahmad Masood
Talla

Sukurkucewar Huldar diflomaciya tsakanin Amurka da India shi ne labarin da ya mamaye daukacin jaridun India bayan da Jami’an tsaron Amurka suka cafke wata babbar Jami’ar diflomasiyar India a birnin New York akan muzgunawa wata mai yi mata hidimar gida tare da kuma batun Visa, takardar izinin shiga kasar ta jabu da ta yi karya akan kudaden da ta ke biyan ma'aikaciyar.

Hakan ne ya sa ita ma gwamnatin India ta dauki matakin kwace katin shedar Amurkawa a ofisoshin jekadancin kasar a India. Kuma gwamnatin India tace zata dakatar da duk wasu kayayyaki da ake shigo da su daga Amurka

A makon jiya ne mahukuntan Amurka suka cafke Devyani a birnin New York a lokacin da take kan hanyar kai ‘yayanta makaranta akan batun kudaden da ta ke biyan wata mai yi mata hidimar gida.

Tun a ranar Juma’a ne gwamnatin India ta kira jekadanta a Amurka domin kalubalantar matakin na Amurka

Amma Wannan shi ne ya tayar da batun muzgunawa masu hidimar gida a kasar India na rashin biyansu kudaden da suka dace. Inda masu kare hakkin bi’adama suka ce ana cin zarafinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.