Isa ga babban shafi
Rasha-Syria-Amurka

Obama: Dole sai Rasha ta lallashi Syria

Shugaban Amurka Barack Obama yace Rasha ce ke da alhakin tabbatar da cewa Syria ta miƙa dukkannin makamanta masu guba domin lalata su ƙarkashin yarjejeniyar da ƙasashen duniya suka ƙulla ta tanada.

Mutanen garin Homs da ake ƙoƙarin ficewa da su daga yankin
Mutanen garin Homs da ake ƙoƙarin ficewa da su daga yankin REUTERS/Thaer Al Khalidiya
Talla

Obama yace kawo yanzu kaɗan daga cikin irin waɗannan makamai ne Syria ta bai waƙasashen duniya, saɓanin ton 700 da ya kamata Syria ta bayar a daidai wannan lokaci.

Sai dai jakadan kasar Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya Vitaly Churkin yace aikin mika makaman na tafiya kamar yadda aka tsara.

Ana sa ran ƙungiyoyin agaji za su ci aba da aikin kwashe mutane a yankin Homs da ke fuskantar hare hare bayan dakatar da aikin na kwanki daya.

Ɗaruruwan mutane ne suka maƙale a birnin na Homs wanda shi ne cibiyar zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Bashar al Assad bayan dubban mutane sun fice daga yankin.

Har yanzu dai babu wani ci gaba da aka samu a tattaunawar da ake yi tsakanin wakilan gwamnatin Syria da Ƴan adawa a Geneva inda aka shiga kwana na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.