Isa ga babban shafi
Libya

Libya na neman izinin sayo makamai

Kasar Libya ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta ba ta damar sayen makamai don magance barazanar kungiyoyin ‘yan ta’addan da suka addabi kasar. Jakadan Libya a Majalisar, Ibrahim Dabbash, ya gabatarwa kwamitin sulhun bukatunsu don ganin an gaggauta amincewa da ita domin ceto Libya daga hannun ‘yan ina-da-kisan da yanzu haka ke cin karen su babu babbaka.

Askarawan Libya da ke fada da mayakan sa-kai
Askarawan Libya da ke fada da mayakan sa-kai REUTERS/Stringer
Talla

Bukatun na Libya sun hada da sayen jiragen yaki 14 da ake kira MIG Fighter jets, helicoftoci 7 da tankuna yaki 150 da kuma motocin sulke masu dauke da bindigogi 150 da na’urar harba gurneti 10,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.