Isa ga babban shafi
Tunisia

Ana gangamin kyamar ayyukan ta’addanci a Tunisia

Dubban mutanen Tunisia sun hada gangami a yau Lahadi domin nuna adawa da ayyukan ta’addanci a kasar musamman kisan gillar da aka yi wa wasu ‘Yan yawon bude ido na kasashen waje a gidan Tarihin kasar.

Shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi da Francois Hollande na Faransa da Shugaban Falasdinawa  President Mahmoud Abbas a gangamin adawa da ta'addanci a Tunis
Shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi da Francois Hollande na Faransa da Shugaban Falasdinawa President Mahmoud Abbas a gangamin adawa da ta'addanci a Tunis REUTERS
Talla

Mahukuntan Tunisia sun ce an yi nasarar kashe Lukman Abu Sakr wanda ya jagoranci harin da aka kai a gidan tarihi, da kuma wasu mabiyansa guda 8.

Tunisia na zargin Abu Sakr ne da mayakansa da laifin kai hari a gidan Tarihin Bardo duk da cewa Kungiyar IS ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin inda aka kashe ‘Yan yawon bude 21 ‘yan kasashen waje.

Hukumomin Tunisia sun ce kungiyar Abu Sakr ta Okba Ibn Nafaa ta dade tana kai wa Jami’an tsaro hare hare inda suka kashe sama da 60 tun a 2012.

A yau Lahadi kuma dubun dubatar al’ummar Tunisia ne suka hada gangami a birnin Tunis dauke da tutar kasar suna yayata kalaman adawa da Ta’addanci.

Shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi ne ya jagoranci gangamin, kuma akwai manyan shugabannin kasashen Turai da suka shiga gangamin wadanda suka hada da Shugaban Faransa Francois Hollande, da shugaban Poland Bronislaw Komorowski, sannan akwai shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas.

Akwai kuma wakilai daga kasashen Italiya da Spain da Holland da Belgium da Rasha da Australia da Birtaniya da kuma Colombia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.