Wata bakar fata ta cire tutar wariyar launin fata a Amurka
A Kasar Amurka, Wata mata bakar fata mai suna Bree Newsome ta cire tutar dake nuna wariyar launin fata da aka kafa a gidan gwamanti dake jihar kudancin Carolina.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tuni dai hukumomi suka cafke Newsome bayan ta sauko daga inda aka kafa tutar.
Ana ta yada hotunan Newsome mai sekaru 30 a shafukan sada zumunta, inda aka nuna ta a hannun hukuma kuma tuni aka mayar da tutar bagirenta.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani matashi farar fata mai suna Dylaan Roof ya harbe har lahira bakaken fata 9 dake ibada a wata mujami’a dake kudancin Carolina na Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu