Isa ga babban shafi
Vatican

Paparoma ya yi jawabi gaban Majalisar Dokokin Amurka

Shugaban Darikar katolika na duniya Paparoma Francis dake ziyarar aiki a kasar Amurka a yau alkhamis ya yi jawabi a gaban Majalisar Dokokin kasar inda ya tabo batutuwa da dama da suka shafi rayuwar al’ummar duniya baki daya

Paparoma Francis
Paparoma Francis REUTERS/Tony Gentile
Talla

Wannan dai shine karon farko da wani shugaban darikar katolika ke kafa irin wannan tarihin a kasar Amurka
A yayin jawabin da Paparoma Francis ya yi na tsawon mintuna arba’in, ya yi kira na kara kaimi wajen magance matsalolin dake tattare da masu tsatsauran ra’ayin addini.

Akwai kuma batun sauyin yanayi da shugaban ya ya yi bayani akai inda ya yaba da irin matakin da wasu kasashen duniya ke dauka na ganin an shawo kan matsalar dake barazana ga rayuwar al’ummar duniya.

A lokacin da yake Magana da ya shafi auren jinsi guda da kasar ta amince da shi kuwa, Paparoma yace samuwar iyali muhinmin abune a ci gaban kowacce kasa al’amarin da ya matukar ratsa zukatan dubban al’ummar kasar dake sauraren jawabin.

Sai kuma batun ‘Yan gudun hijra da Paparoma ya shawarci Amurka da ta taimakawa bayin Allah dake gujewa tashe tashen hankula a kasashen su inda yace a duba matsalolin da suke ciki maimakaon mayar da hankali akan yawan ‘Yan gudun hijrar dake tururuwa zuwa kasashen Turai.

Wannan dai shine karo na farko da Paparoma Francis mai shekaru 78 a duniya ke kai ziyarar a kasar Amurka tun bayan zama shugaban darikar cocin katolika a duniya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.