Isa ga babban shafi
Saudi

Paparoma zai gabatar da Jawabi a zauren MDD

Shugaban darikar Katolika ta duniya, Paparoma Francis zai gabatar da jawabinsa na farko a zauren Majalisar Dinkin Duniya a yau Jumma’a, inda zai yi kira ga Shugabannin duniya game da muhimman batutuwa.

Shugaban darikar katolika ta duniya Paparoma Francis.
Shugaban darikar katolika ta duniya Paparoma Francis. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Paparoma zai bukaci Shugabannin Kasahen duniya da su taimakawa Talakawa da kuma yaki da matsalar sauyin yanayi harma da kawo karshen tashe tashen hankulan da suka yi sanadiyar kwararar 'yan gudun hijira cikin nahiyar Turai.

A karon farko za a daga tutar fadar Vatican a Shalkwatan Majalisar Dinkin Duniya saboda wannan zama na yau wanda kuma zai samu halartar Paparoma a karo na biyar cikin shekaru 70.

Jawabin na Paparoma ga zauren dake kunshe da kasashe 193 na zuwa ne a daidai lokacin da Kasar Amurka ta kasa kai ga gaci wajan kawo karshen tashe tashen hankulan dake faruwa a Kasar Syria.

Sama da mutanen Syria miliyan 4 suka kauracewa gidajensu sakamakon rikicin Kasar, abinda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin al-amarin da ya haifar da 'Yan gudun hijra mafi yawa a tarihi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.