Za mu murkushe shugaban IS- Obama
Shugaban Amurka Barack Obama ya sha alwashin kwato yankunan da mayakan IS masu da’awar Jihadi suka kwace a gabas tsakiya tare da shan alwashin kashe shugabansu.
Wallafawa ranar:
Obama ya fadi haka ne bayan ya zanta da manyan Jami’an tsaron Amurka.
Shugaba Obama ya ce Amurka da kawayenta sun karbi aikin yaki gadan gadan da IS a Iraqi da Syria.
Ya kuma bayyana wasu shugabannin mayakan IS guda 8 da aka kashe a hare haren da aka kai wa mayakan. Sannan Obama yace yanzu Shugaban IS ne a gabansu da za su kashe.
Amurkawa dai na ganin Obama na tafiyar hawainiya ga yaki da IS, bayan harin da aka kai a San Bernardino a California.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu