Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya kare manufofin gwamnatin shi a Amurka

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kare manufofin gwamnatin shi a jawabin karshe ga majalisun dokokin kasar inda ya bukaci Amurkawa su rungumi canji tare da cire fargaba musamman ga barazanar tsaro da tattalin arziki.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Evan Vucci/Pool
Talla

Shugaba Obama ya zargi masu sukar manufofinsa a matsayin magoya bayan kungiyar IS, yana mai cewa yaki da kungiyar ba shi ne yakin duniya na uku ba.

Mista Obama ya fadi haka ne a jawabin shi na karshe da ya gabatar a majalisun dokokin Amurka wanda ya sabawa tunanin ‘Yan Jam’iyyar Republican da ke sukar gwamnatinsa.

Sannan, Obama ya yi watsi da barazanar Kungiyar IS ga Amurka, inda ya ce kasar na da karfin tsaron da za ta iya murkushe duk wata barazanar ‘Yan ta’adda.

Sannan shugaban ya ce babu gaskiya a zargin cewar tattalin arzikin Amurka na komawa baya, ko kuma kasar na gazawa a fagen siyasar duniya kamar yadda masu neman kujerarsa daga Jam’iyar Republican ke bayyanawa.

Shugaban ya yi bayani kan yunkurin kasar na ganin ta zama inda ake warkar da cutar kansa a duniya, tare da bayyana mataimakinsa Joe Biden a matsayin wanda zai jagoranci aikin.

Obama ya bukaci majalisar kasar ta kawar da bambamcin da ke tsakaninsu na siyasa don aiwatar da sauye sauyen da za su taimaki Amurkawa, musamman dokar takaita mallakar bindiga.

A yayin da ya ke mayar da martani ga kalaman Donald Trump dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar Republican kan Musulmi, Shugaba Obama ya bukaci Amurkawa su dai na kin jama’a saboda addinin su ko kabilarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.