Isa ga babban shafi
Brazil

Magoya bayan Lula na Brazil sun damu

Magoya bayan tsohon shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva na nuna damuwarsu kan yadda aka gurfanar da shi a gaban shari’a saboda tuhumar da ake masa na halarta kudaden haramun.

Shugabar kasar Brazil Dilma Roussef da tsohon shugaban kasar Inacio Lula da Silva.
Shugabar kasar Brazil Dilma Roussef da tsohon shugaban kasar Inacio Lula da Silva. REUTERS/Joedson Alves
Talla

Masu gabatar da kara na zargin tsohon shugaban ne da mallakar wasu gidajen alatu a gabar ruwan Sao Paolo da Guaruja.

Ita dai wannan shari’a ta tsohon shugaban kasa Inacio Lula da Silva na da matukar tasiri a siyasar kasar, ganin yadda al’ummar Brazil ke girmama tsohon shugaban nasu saboda rawar da ya taka wajen daga darajar Brazil da kuma bunkasa tattalin arzikinta, inda ta zama daya daga cikin manyan kasashen duniya 5 da arzikinsu yafi habbaka.

Masu gabatar da karar sun dade suna zargin Lula da wasu jami’ansa da suka hada da shugabar kasar mai ci Dilma Rousseff da karbar na goro domin bada kwangila a katafaren kamfanin man kasar Petrobras.

Masu sa ido na kallon tuhumar da ake yi wa Lula a matsayin matakin farko na kai wa ga shugaba Rousseff wadda majalisar kasar ke ta kokarin tsige ta saboda zargin da suke ma ta na hannu a badakalar cin hanci.

Yanzu dai hankali ya koma kan alkalin da aka gabatar da zargin a gabansa, na amincewa da tuhumar ko kuma watsi da ita.

A baya dai an daure wasu jami’an tsohon shugaban.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.