Jagorar Democradiyya na Kasar Myanmar Na Asibiti Saboda Matsalar Ido
Jagorar masu kishin kafuwar Democradiyya a kasar Myanmar Uwargida Aung Sang Suu Kyi na kwance a wani Asibitin Idanu saboda matsalar ciwon ido da take fama dashi.
Wallafawa ranar:
‘Yar shekaru 70, kafofin labaran kasar sun nuna ta a Asibiti, wani likita mai suna Tin Myo Win na duba lafiyar idanun ta, kuma shine ke cikin mutane ‘yan kalilan da sojan kasar suka bari ya rika ziyartar ta a lokacin da take tsare a gidan ta na tsawon shekaru 15.
Uwargida Aung San Suu Kyi na rike da mukamin Ministan Harkokin kasashen waje na kasar.
Majiyoyi na cewa za’ayi mata aiki a idanun ta ranar 16 ga wannan wata da muke ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu