Isa ga babban shafi
Faransa-Masar

Hollande ya kulla yarjeniyoyi da al-Sisi

Shugaban Faransa Francois Hollande ya kulla yarjeniyoyi da dama da takwaransa na Masar Abdel Fatah al Sisi a ziyarar kasae da ya kai wadda ta gamu da suka daga kungiyoyin kare hakin bil Adama.

Shugaban Masar Abdel Fatah al- sisi da takwaransa na Faransa, Francois Hollande
Shugaban Masar Abdel Fatah al- sisi da takwaransa na Faransa, Francois Hollande REUTERS/Etienne Laurent/Pool
Talla

Shugaba Hollande da Abdel Fatah al- Sisi sun jagoranci sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama, cikin su har da na Euro sama da biliyan guda don fadada hanyoyin jirgin kasa a birnin Alkahira.

A taron da suka yi da manema labarai, shugabanin biyu sun yi bayani kan zargin cin zarafin bil Adama da ake yi wa shugaban na Masar, inda al-Sisi ya ce Hollande ya tabo maganar a ganawar da suka yi, inda ya shaida masa cewar yankin da Masar ta ke na fama da tashin hankali.

Al- Sisi ya ce bai dace ace za ayi amfani da mizanin kwatanta ‘yancin bil Adama a Turai da yadda abin yake a kasashen dake fama da tashin hankali irin su Masar ba.

A nashi jawabi, shugaba Hollande wanda ya samu kyakyawar tarba daga mai masaukin nasa ya ce, kare hakkin bil Adama ba zai zama tarnaki wajen yaki da ta’addanci ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.