Isa ga babban shafi
Syria

Kauracewar ‘Yan adawar Syria a Geneva matsala ce- Hollande

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce matakin da ‘Yan adawar Syria suka dauka na kauracewa zaman sansanta rikicin kasar a Geneva babbar damuwa ce ga kokarin kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru biyar ana zubar da jini.

Shugaban Faransa Francois Hollande a Fadar Sarki Abdallah na Jordan
Shugaban Faransa Francois Hollande a Fadar Sarki Abdallah na Jordan REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Shugaban ya bayyana damuwar ne kwana guda bayan ‘Yan adawar Syria sun dauki matakin kauracewa taron Geneva.

Hollande ya ce wannan babbar damuwa ce ga yarjejeniyar tsagaita wuta da ta taimaka aka samu sassaucin yaki a wasu sassan Syria.

Hollande ya fadi haka ne a ganawar shi da Sarki Abdallah na Jordan, yana mai cewa idan har aka rusa yarjejeniyar tsagaita wuta to rikici zai dawo wanda zai haddasa kauracewar mutane a gidajensu.

Hollande ya ce tattaunawar Geneva na da matukar muhimmaci ga kokarin da ake na kawo karshen rikcin Syria.

A ranar Litinin ne dai manyan kungiyar ‘yan adawar Syria suka sanar da kauracewa zaman taron Geneva bayan sun zargi dakarun gwamnatin Shugaban kasar Bashar Al Assad da kai hare hare a yankin Alepoo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.