Isa ga babban shafi
Syria

Dole Assad ya sauka- inji Obama

Shugaban Amurka Barack Obama wanda ke gabatar da jawabi a gaban taron shugabannin kasashen Larabawan yankin Gulf, ya ce dole ne Bashar Assad ya sauka daga kan mukaminsa na shugabancin kasar Syria.

Shugban Syria Bashar al-Assad
Shugban Syria Bashar al-Assad JOSEPH EID / AFP
Talla

Obama wanda ya kai ziyarar aiki ta yini biyu a kasar Saudiyya, ya ce a matsayin Assad na shugaban da ya zubar da jini, bai kamata a bar shi a matsayin shugaba ba.

Obama ya ce babban dalili, wanda kuma suke jaddadawa kan dole Assad ya sauka daga mukaminsa shi ne, na farko dai yana kashe al’ummarsa, yana kashe mata har ma da kananan yara.

Zai kasance abu mai wuya a bar irin wannan mutum a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin kasa, sannan kuma a yi hasashen cewa zai iya kawo karshen yakin da ke faruwa a cewar Obama.

Dubban mutane suka mutu a rikicin Syria tare da tursasawa Miliyoya barin gidajensu a tsawon shekaru biyar da aka shafe ana yaki a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.