Isa ga babban shafi
Brazil

Rousseff ta ce tsige ta barazana ce ga demokradiya

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana matakin dakatar da ita a mastayin babban barazana ga makomar demokradiyar kasar.

Shugabanr kasar Brazil Dilma Rousseff
Shugabanr kasar Brazil Dilma Rousseff REUTERS/Adriano Machado
Talla

Kallaman Rouseff na zuwa ne, bayan Kuri’ar da Majalissar dattijen kasar suka kada, wanda ya bayar da daman dakatar da ita don fuskantar tuhuma kan batun cin hanci da rashawa.

Rousseff, mace ta farko data shugabanci Brazil, samun ta da laifi zai kawo karshan mulkin masu sassauci ra’ayi da suka kwashe tsawon shekaru 13 suna tafiyar da kasar dake latin Amurka.

A yanzu dai mataimakin ta Michel Temer ne ya maye gurbin ta na tsawon watanni shida da Rouseff zata fuskanci shari’ar, wanda dama take zargi shi da hannu a yunkurin kifar da ita.

Rousseff da magoya bayanta sun soki wannan mataki da suka danganta da juyin mulki ‘yan adawa, inda suka ce daman tun asali ana bibiyanta da bita da kullin siyasa.

A na zargin Rousseff ne da boye gagarumin gibi a asusun kasar gabanin sake zaben ta a shugabar kasar a shekarar 2014, sai dai ta sha musanta zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.