Isa ga babban shafi
Birtaniya

Brown na Birtaniya zai tallafa wa 'yan gudun hijira

Tsohon firaministan Birtaniya Gordon Brown ya kaddamar da wani asusu don neman kudin tallafa wa kananan yaran ‘yan gudun hijira kusan miliyan 30 da wata kididdiga ta nuna cewa basa zuwa makaranta sam-sam.

Wasu daga cikin yaran 'yan gudun hijira.
Wasu daga cikin yaran 'yan gudun hijira. SAKIS MITROLIDIS / AFP
Talla

Asusun mai taken "Ilimi baya jiran wani" na bukatar tara kudi har Dalar Amurka kusan biliyan hudu cikin shekaru biyar daga hannun gwamnatoci da manyan kamfanoni da masu hannu da shuni.

A makon gobe ake saran za a kaddamar da wannan asusu a birnin Istanbul na Turkiya, inda za a yi taron kasa da kasa game da ayyukan jin kai.

Mr. Brown ya ce, daukan nauyin yaran 'yan gudun hijirar Syria da ke zaune a sansanonin Jordan da Turkiya da Lebanon  domin zuwa  makaranta, zai lakume Dala miliyan 800 a duk shekara.

A bangare guda, kimanin kananan yara miliyan 75 ne a duk fadin duniya suka katse zuwa makaranta saboda yake yake da sauran ibtila'oi daban daban.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.