Isa ga babban shafi
Amurka-Faransa

Amurka ta sauke tutocinta saboda harin Faransa

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar umarnin yin kasa da tutocin kasar don nuna jimami ga harin da aka kai birnin Nice na Faransa, inda mutane 84 suka rasa rayukansu.

Shugaba Hollande na Faransa da takwaransa Obama na Amurka
Shugaba Hollande na Faransa da takwaransa Obama na Amurka 路透社
Talla

Shugaba Obama ya kuma kira takawaransa na Faransa Francois Hollande ta wayar tarho inda ya yi masa jaje kan kazamin harin da Mohamed Lahouaiej Bouhlel ya kai kan jama’ar da ke halartar bikin ranar samun ‘yancin kan kasa a jiya Alhamis.

Mai magana da yawun fadar White House Josh Ernest ya ce, Amurka ta bai wa mahukuntan Faransa duk taimakon da suke bukata don gudanar da bincike kan lamarin.

Obama ya danganta harin da ta’addanci kuma ana saran zai gabatar da jawabi in anjima akan batun a gaban manyan jami’an diflomasiyya a fadarsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.