Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na zaman makoki bayan harin ta'addanci a Nice

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya sanar da zaman makoki na kwanaki 3 bayan  kazamin harin da wani direba ya kai da mota kan masu bikin ranar Yancin kan kasar da ya kashe mutane sama da 80.

Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 80 a birnin Nice
Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 80 a birnin Nice REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Yayin jawabi ga al’ummar kasar shugaba Hollande ya bayyana tsawaita dokar ta bacin dake shirin karewa na watanni uku inda ya ce wannan wani harin ta'addancin ne aka sake kaiwa Faransa.

Shugaba Francois Hollande cikin halin kaduwa yace an kai wannan hari ne a ranar da Faransawa ke bikin ranar yancin kan su, kuma cikin wadanda harin ya ritsa da su har da kananan yara.

Hollande ya bayyana damuwa kan yadda za’ayi amfani da mota dan hallaka wadanda ke walwalar su, inda yake cewa kasar ba zata bada kai bori ya hau ba, a yaki da ta’adanci da kuma karfafa aikin da suke a Iraqi da Syria wajen yaki da ISIS.

Shugaban ya sanar da kara wa’adin dokar ta baci na watanni uku da kuma kiran sojin wucin gadi dan inganta tsaro a kasar.

Hollande yace zasu ci gaba da kai hari kan wadanda suka kawo musu hari a kasar su.

Wannan dai shine hari na uku cikin watanni 18 a kasar, kuma yana zuwa ne sa’oi kadan bayan shugaban kasar yace ba zasu tsawaita dokar ta bacin da ke shirin karewa ranar 26 ga wata ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.