Isa ga babban shafi
France

Ana ci gaba da bincike kan harin Faransa

Hukumomin Faransa sun bayyana Mohamed Lahouaiej Bouhlel a matsayin matashin da ya kai harin ta’addanci kan jama’ar da ke murnar bikin ranar samaun ‘yan cin kasar.

Motar da maharin ya yi amfani da ita wajen kai a birnin Nice na Faransa tare da kashe mutane fiye da 80
Motar da maharin ya yi amfani da ita wajen kai a birnin Nice na Faransa tare da kashe mutane fiye da 80 REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Hukumomin sun ce an haifi matashin ne mai shekaru 31 a kasar Tunisiya amma yana zaune a Faransa.

Bayan gano hakikanin matashin wanda ya kashe mutane fiye 80 a harin na jiya a birnin Nice, a halin yanzu hukumoimin Faransa na tuhumar tsohuwar matarsa bayan sun an cafke ta dazin nan.

Masu binciken na bukatar karin haske game da dabi’un maharin da kuma sanin ko akwai wadanda suka taimakasa wajen kai harin da katuwar mota, inda ya murkushe jama’a tare da harbe wasu har lahira.

Tuni dai aka tabbatar da mutuwarsa bayan jami’an tsaro sun bude masa wuta.

Makwabtan maharin sun bayyana shi a matsayin muskilin mutum da baya amsa gaisuwa.

A bangare guda, shugaban kasar ta Faransa, Francois Hollande ya ce, a halin yanzu akwai mutane kimanin 50 da ke cikin halin mutu kwa-kwai- rai -kwa-kawai.

Sannan ya ce, akwai baki ‘yan kasashen katare da kananan yara da kazamin harin ya yi sanadiyar ajalinsu.

Amurka da Ukraine duk sun ce akwai ‘yan kasashensu da lamarin ya ritsa da su.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.