Isa ga babban shafi
US

Wutar daji ta fitar da mutane daga gidajensu a Amurka

Mahukuntan jihar California ta Amurka sun bayyana cewa, wata gobarar daji mai saurin gaske ta tilasta wa daruruwan mazauna yankin arewacin Los Angeles kaurace wa gidajensu.

Wutar daji ta tilasta wa daruruwan mutane a Los Angeles na Amurka
Wutar daji ta tilasta wa daruruwan mutane a Los Angeles na Amurka REUTERS/Mark Blinch/File Photo
Talla

Wutar dajin ta mamaye kimanin eka dubu 20 a yammacin jiya Asabar, lamarin da ya haddasa tirnikewar hayaki a wasu sassan birnin na Los Angeles.

Kimanin ‘yan kwana-kwana 900 ne tare da taimakon jiragen sama masu saukan ungulu ke ci gaba da kokarin kashe wutar dajin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.