Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta kashe masanin Nukiliya

Iran ta kashe wani masanin Nukiliyarta wanda aka kama da laifin mika wa Amurka wasu bayanan sirrin kasar. An kashe malamin mai suna Shahram Amiri ta hanyar rataya.

Masanin Nukiliyar Iran Shahram Amiri da aka kashe
Masanin Nukiliyar Iran Shahram Amiri da aka kashe Reuters/路透社
Talla

Amiri dai shi ya dawo da kansa a Iran a 2010 bayan ya gudu zuwa Saudiya.

Sai dai kuma gwamnatin Iran ta ki amincewa da bayanansa akan Jami’an Amurka ne suka yi garkuwa da shi domin tatsar bayanan sirrin kasar.

Iran ta katse huldar diflomasiya da Amurka lokacin da dalibai suka abkawa ofishin jekadancin Washington a Tehran a 1980 bayan juyin juya hali na musulunci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.