Amurka da Rasha na sabunta Makaman Nukiliya
Wani Bincike ya nuna cewar Amurka da Rasha manyan kasashen duniya da suka mallaki makaman nukiliya na rage yawan makaman da suka mallaka a hankali, amma kuma a bangare daya suna sabunta wadanda suke da shi domin tafiya da zamani.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Binciken da kungiyar tabbatar da zaman lafiya mai cibiya a Stockholm ta gudanar ya nuna cewar, kasashe 9 da suka kunshi Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa da India da Pakistan da Israila da kuma Koriya ta arewa na da makaman nukiliya 15,395 a farkon wannan shekara cikin su har da 4,120 da aka girke su.
Rahotan kungiyar yace an samu raguwar kera makaman tun a tsakiyar shekarar 1980 lokacin da ake da 70,000 sakamakon amincewar Amurka da Rasha na rage wadanda suka mallaka.
Kungiyar tace kasashen biyu yanzu na tafiya a hankali wajen rage makaman sabanin yadda suka fara shekaru 10 da suka gabata.
Kungiyar ta ce a farkon wannan shekarar ta 2016 Rasha na da makaman nukiliya 7,290 yayin da Amurka ke da 7,000 wanda ke nuna cewar kasashen biyu na da kashi 93 na makaman nukiliya a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu