Isa ga babban shafi
Amurka-Philippines

Duterte ya bayyana Obama a matsayin ‘dan karuwa’

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya soke ganawar da ya shirya yi da shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte bayan zagin da ya masa a wasu kalamai masu zafi.

Shugaban kasar Philippin Rodrigo Duterte
Shugaban kasar Philippin Rodrigo Duterte REUTERS/Lean Daval Jr
Talla

Duterte kafin tashin sa zuwa wajen taron shugabanin kasashen Asia da Pacific ya ce ba zai bai wa Obama damar yi masa huduba kan kare hakkin Bil Adama ba sakamakon yakin da ya kaddamar na kashe masu safarar miyagun kwayoyi.

Shugaban na Philippines ya bayyana Barack Obama a matsayin ‘dan karuwa’ kalaman da suka sa fadar sa ta soke ganawar shugabanin biyu.

Tuni dai wannan batu ya dau hankali duniya inda ake ci gaba da mayar da martani kan kalaman Duterte.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.