Isa ga babban shafi
Saudiya

Alhazai sun fara fita garin Makkah zuwa Mina

Maniyata aikin Hajji bana kusan miliyan biyu sun soma fita garin Makkah zuwa Mina, mataki na farko na fara aikin Hajji kafin zuwa Arfa ranar lahadi.

Masallacin Harami da ke Saudiya
Masallacin Harami da ke Saudiya Wikimedia Commons
Talla

Rahotanni daga Makkah sun ce garin ya yi cikar kwari da dubun dubatan maniyata wadan da ke shirin gudanar da aikin Hajjin bana.

Ganin yadda zafi rana ya zarce maki 40 na mazaunin yanayi, da kuma cikar mutane a Masallacin Makkah, hukumomin Saudiya sun dada inganta Masallacin da kuma sanya masa na’urar sanyaya gida da kuma kayata haramin.

Hukumomin kuma sun karfafa matakan tsaro dan tabbatar da cewar an magance duk wata barazana da ke iya tasowa.

Hadarin da aka samu bara bai sanyaya gwiwar al’ummar Musulmi cika birnin na Makkah ba dan gudanar da ibada.

Sai dai, a dai-dai lokacin da ake fara aikin Hajjin cacar baki ya kaure tsakanin Iran da Saudiya, inda Iran ta bukaci Musulmin duniya su kalubalanci Saudiyar kan yadda ta ke tafiyar da aikin Hajjin, matakin da ya sa daya daga cikin manyan malaman kasar ya ce ai mutanen na Iran ba Musulmi bane.

Saudiya dai ta hana maniyatan Iran 60,000 zuwa aikin Hajjin bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.