Isa ga babban shafi
Colombia

Zaben raba gardama dangane da shirin zaman lafiyar Colombia

An fara kada kuri’a domin jin ra’ayin al’ummar kasar Colombia dangane da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin gwamantin kasar da kuma ‘yan tawayen FARC wadda ta kawo karshen yakin basasar shekaru 52 a kasar.

Shugaban Colombia Juan Manuel Santos da shugaban FARC Timochenko bayan sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
Shugaban Colombia Juan Manuel Santos da shugaban FARC Timochenko bayan sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya Luis ACOSTA / AFP
Talla

Shugaban kasar ta Colombia Juan Manual Santos, ya ce ba ya da wani zabi matukar dai al’ummar kasar suka yi watsi da wannan jituwa a zaben na yau.

Yakin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawayen FARC, shi ne mafi muni a yankin na Latin Amurka, inda ya yi sanadiyyar mutuwar dubun dubatar mutane a tsawon shekaru 52.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.