'Yan tawayen FARC sun mika sojoji yara ga gwamnatin Colombia
Kungiyar ‘Yan tawayen FARC ta kasar Columbia, ta mika tawagar farko ta sojoji kananan yara ga gwamnatin kasar, a matsayin fara cika alkawarin da ta dauka bayan cimma yarjejeniyar ajiye makamai tsakaninta da gwamnati.
Wallafawa ranar:
Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta ce za’a fara tura yaran guda takwas asibiti, domin duba lafiyarsu kafin mika su ga iyalansu, daga bisani kuma a tura su zuwa cibiyar da gwamnatin kasar ta tanada domin gyaran halayya.
‘Yan tawayen na FARC da suka ajiye makami a watan da ya gabata, sun ce akwai yara da aka tilastawa shiga aikin soja 21 a karkashinsu, kuma tun a waccan lokacin suka yi alkawarin mika su ga gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu