Columbia
Za a yi bikin cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Colombia
A ranar 26 ga watan Satumba ne, gwamnatin Colombia za ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar ‘yan tawayen FARC a hukumnce, kamar yadda shugaban kasar, Juan Manuel Santos ya sanar.
Wallafawa ranar:
Talla
Mr. Santos ya ce, sanarwar cimma yarjejeniyar da nufin kawo karshen rikicin shekeru 50, ita ce mafi muhimmanci a rayuwarsa.
Shi ma shugaban ‘yan tawayen, Timoleon Timochenko ya sanar da ranar cimma yarjejeniyar a shafinsa na Twitter.
A na saran shugabannin kasashen yankin Latin Amurka za su halarci bikin cimma yarjejeniyar wanda za a yi a birnin Cartagena.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu