Colombia zata dakatar da kai hari kan yan FARC
Shugaban Kasar Colombia Juan Manuel Santos yace sojojin kasar zasu daina kai hari kan ‘Yantawayen kungiyar FARC a yunkurin kawo karshen yakin basasa mafi tsayi a Yankin Amurka ta kudu. A sanarwar da ya yi ta kafar Talabijin, shugaban ya ce ya umurci Ministan tsaron kasar da kwamandojin soji da su daina kai hari kan sansanin ‘yantawayen.
Wallafawa ranar:
Akalla mutane 220,000 ne aka kashe a yakin da Dakarun kasar ta Colombia ke yi da ‘yan tawayen FARC masu dauke da muggan makamai.
Santos ya ce akwai alamun da ke nuna cewar a wannan karon kungiyar FARC na nuna goyon bayan shirin gwamnati, na sasantawa a tsakaninsu da kuma samar da zaman lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu