Isa ga babban shafi
Faransa

Birtaniya ce za ta kwashe bakin Calais na Faransa

Gwamnatin Faransa ta bayyana cewa, Birtaniya ce ke da alhakin kwashe ‘ya’yan ‘yan gudun hijira da ke jigbge a dajin Calais, kuma wannan na zuwa ne bayan kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta caccaki Birtaniya saboda jan kafar da ta ke yi wajen kwashe bakin. 

Sansanin 'yan gudun hijira na Calai da ke Faransa
Sansanin 'yan gudun hijira na Calai da ke Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve ya bayyana cewa, zai matsa lamba kan wannan batu a zaman cin abincin rana da zai yi da takwaransa na Birtaniya, Amber Rudd a birnin London.

A wata hira da ya yi da gidan rediyon RTL, Mr. Cazeneuve ya ce, akwai daruruwan yaran ‘yan gudun hijira masu dangi a Birtaniya da ke zaune a dajin na Calais, abin da ya sa ya bukaci Birtaniya ta dauki nauyinsu.

Kimanin mutane dubu 10 ne ke samun mafaka a dajin, kuma akasarinsu sun kaurace wa tashe-tashen hankula ne a Syria da Afghanistan da kuma nahiyar Afrika, in da suke burin tsallakawa Birtaniya.

A jiya Lahadi ne, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta soki Birtaniya saboda yadda ta yi watsi da sha’anin daruruwan yaran bakin, wadanda kuma ke da hakkin saduwa da danginsu a Birtaniyar.

To sai dai mai magana da yawun gwamnatin Birtaniya ya ce, suna aiki da Faransa don gaggauta tsara yadda za a fara kwashe ‘yan gudun hijirar.

A cikin mako mai zuwa ne, ake zaton cewa, Faransa za ta fara aikin wargaza sansanin Calais, inda za a sauya ‘yan gudun hijirar wuraran zama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.