Isa ga babban shafi
Philippines

An kashe wani magajin gari a Philippine

An kashe wani magajin gari a Philippine da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi tare da wasu masu tsaron shi guda 9 a wata musayar wuta da ‘yan sanda a yau Juma’a. wannan na zuwa bayan shugaba Rodrigo Duterte ya yi barazanar kara kaimi ga yaki da masu safarar miyagun kwayoyi.

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya kaddamar da yaki da masu safarar kwayoyi bayan zaben shi shugaban kasa
Shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya kaddamar da yaki da masu safarar kwayoyi bayan zaben shi shugaban kasa REUTERS
Talla

Samsudin Dimaukom magajin garin Saudi Ampatuan na cikin jami’an gwamnati 150 da suka hada da Alkalai da ‘Yan sanda wadanda shugaba Duterte ke zargi na safarar mayagun kwayoyi.

‘Yan sandan Philippine sun ce jami’an tsaron da ke tsaron magajin garin ne suka fara bude wuta bayan an tsayar da su domin gudanar da bincike akan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Sama da mutane 3,800 aka kashe a yaki da safarar miyagun kwayoyi da shugaba Duterte ya kaddamar a Philippine, wanda ke ci gaba da shan suka daga Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.