Isa ga babban shafi
Amurka

Mukarraban Trump na yi wa Obama fatan Mutuwa

Daya daga cikin mukarraban shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, na fuskantar suka da tofin ala tsine, bisa kalaman da ya yi, na fatan mutuwar Barrack Obama, da kuma batanci ga matarsa Mitchel.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama REUTERS/Carlos Barria
Talla

Carl Paladino, wanda sanannen dan kasuwa ne, ya yi wannan katobara ce, yayin zantawarsa da wata jarida da ake wallafawa a birnin New York na Amurka.

Paladino wanda shi ne mataimakin shugaban yakin neman zaben Trump a Birnin New York, ya yi wannan barin zance ne a lokacin da jaridar ta tambaye shi game da abinda yake fatan ganin ya faru a shekara ta 2017.

Paladino ya ce fatansa shi ne shugaban Amurka, Barrack Obama, ya kamu da cutar haukar shanu bayan an kamashi da laifin tarawa da saniya, kafin kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

A game da Mitchel Obama kuma, Paladino cewa ya yi, yana fatan matar shugaban kasar ta koma da namiji wanda shi ne  yafi da cewa da ita, ta kuma koma rayuwa da gwaggwon biri a Zimbabwe.

Wadannan barin zance da Paladino ya yi, ya jawo masa tofin ala tsine cike da fusata a kafafen sadarwar zamani.

A martaninsa gwamnan New York, Andrew Cuomo, ya bayyana kalaman Paladino a matsayin masu muni da rashin da cewa, ko da ya ke a cewar Coumo dama Paladino na da tarihin furta irin wadannan kalaman kasancewarsa mai nuna wariyar launin fata.

Ko da dai Donald Trump bai ce komai ba a game da kalaman na hannun damannasa, wata mai Magana da yawunsa ta ce basa goyon bayan halayyar ta Paladino.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.