Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta zargi Rasha da taimakawa Trump lashe zabe

Jaridar Washington Post ta rawaito cewa Hukumar leken asiri ta Amurka CIA, ta ce ta samu hujjoji da suka tabbatar da cewa Rasha taimakawa shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump a nasarar da ya samu ta lashe zaben shugabancin kasar.

Shugaban Amurka Barrack Obama
Shugaban Amurka Barrack Obama
Talla

Jaridar ta ce, jami’an hukkumar ta CIA sun gano wadansu mutane da suke da alaka da gwamnatin Rasha, wadanda da hannunsu wajen yin kutse, da kuma bankado bayanan wasu sakwannin kafar e-mail da aka yi, ciki har da na yar takarar shugabancin Amurka, karkashin jam’iyyar Democrat Hillary Clinton.

Rahoton jami’an leken aisirin ya ce, wadannan mutane sun taka rawa wajen dakushe karsashin Clinton na lashe zaben shugabancin Amurka, yayin da suka taimaki Donald Trump samun nasara.

A watan Oktoba da ya gabata, gwamnatin Amurka ta zargi Rasha yi mata kutse da aleken asiri cikin sakwannin e-mail na wasu ‘yan jam’iyyar Demokrat.

A halin yanzu shugaban Amurka mai barin gado Barrack Obama, ya bawa hukumomin leken asirin kasar umurnin gudanar da bincike kan zargin da ake na taka rawar wata kasa a zabukan Amurka da suka gudana a watan Nuwamba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.