Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya ki danganta ‘yan ta’adda da addinin Islama

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama yayi bayani akan dalilin da ya sa baya danganta ‘yan ta’adda da addinin Islama.

Obama ya ki danganta ‘yan ta’adda da addinin Islama
Obama ya ki danganta ‘yan ta’adda da addinin Islama REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Yayin da yake amsa tambayar wata mata Tina Houchins da aka kashewa ‘da a harin ta’addanci, shugaban yace mutane da kungiyoyin dake kai hare hare suna ikrarin addinin Islama basu da wata dangantaka da addinin.

Shugaban ya bayyana wadannan ‘yan ta’adda a matsayin wadanda suke kashe yara da Musulmai da kuma sace mata wanda babu wani addini da ya amince da haka.

Obama yace sau da yawa idan zai yi magana akan su ya kan yi taka tsan tsan wajen nesanta wadannan mutane da al’ummar Musulmin duniya sama da biliyan guda, cikin su har da wadanda ke Amurka kuma suke cikin sojoji da ‘Yan Sandan kasar da malaman makarantu da masu aikin kashe gobara.

Shugaban yace a matsayin sa na krista ba zai amince wani ya kai harin ta’addanci ya kuma ce shi krista ne ba, domin ba haka addinin yayi horo ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.