Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya gana da Obama a fadar White House

A karon farko zababben shugaban Amurka Donald Trump da kuma shugaba mai barin gado Barack Obama sun gana don soma tsara yadda sabon shugaban zai karbi mulki a watan janairu mai zuwa.

Barack Obama ya gana da Donald Trump.
Barack Obama ya gana da Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Ganawar ta yau dai na zuwa ne kwana daya bayan da aka tabbatar da Trump a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugabancin kasar ta Amurka, bayan ya doke Hillary Clinton da gagarumin rinjaye.

To sai dai wannan nasara ta ba zata da Trump ya yi, ta haddasa barkewar tarzoma a birane da dama na Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.