Isa ga babban shafi

Trump: Hannayen jari sun fadi a duniya

Kasuwannin hannayen jari a duniya sun fadi, sannan darajar kudin Mexico ya yi faduwar da ba a taba gani ba sakamakon rahotannin da ke fitowa daga zaben Amurka saboda nasarar da Dan takarar Republican Donald Trump ya samu nasara akan abokiyar hamayyar shi Hillary Clinton ta Democrat.

Donald Trump na Republican ya lashe zaben Amurka
Donald Trump na Republican ya lashe zaben Amurka REUTERS
Talla

Sakamakon zaben ya na Trump ya samu kuri'un wakilai 288 yayin da Hillary ta samu 215.

Akasarin kasuwannin duniya sun yi fatar ganin Hillary Clinton ta samu nasara, amma yadda sakamakon ya kasance Trump ne akan gaba ya jefa shakku da fargaba tsakanin ‘Yan kasuwar.

Bayani sun nuna cewar a Tokyo, hannayen jarin sun fadi da sama da kashi 5 da rabi, a Hong Kong sun fadi da kusan kashi 3, a Shanghai ma da kusan kashi daya da rabi.

Hannayen jarin Sydney sun fadi kamar yadda suka fadi da kashi biyu da rabi a Seoul da Jakarta da Manila da Bangkok.

Masu ra’ayin rikau irin na Trump daga kasashen Turai sun fara aiko ma shi da sakon taya murna.

Nan gaba kadan ne Donald Trump zai gabatar da jawabi ga dimbin magoya bayan shi a New York kan nasarar lashe zaben da ya girgiza duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.