Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya zabi Gorsuch don cike gurbi a kotun koli

Shugaban Amurka Donald Trump ya zabi Neil Gorsuch a matsayin wanda zai cike gurbin alkalin kotun kolin kasar da aka dade ana takaddama akai.

Neil Gorsuch tare da shugaba Donald Trump na Amurka
Neil Gorsuch tare da shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugaba Trump ya ce, Neil Gorsuch mai shekaru 49 shi ne zai cike gurbin alkalin kotun kolin sakamakon rasuwar Antonin Scalia kusan shekara guda da ta wuce.

Gorsuch wanda ya yi suna wajen iya rubuta hukuncin shari’a, shi ne ya zama alkalin kotun koli mai karancin shekaru da aka taba samu a wannan karnin.

Kokarin maye gurbin Scalia da shugaba Barack Obama ya yi ya ci tura, lokacin da ya gabatar da sunan alkalin kotun daukaka karar Columbia da ke Washington Merrick Garland, amma Trump da 'yan majalisar dattawan jam’iyyar Republican da ke da rinjaye a majalisar suka ki amincewa da nadin.

Jam’iyyar Republican na da wakilai 52 a majalisar dattawan kasar kuma dole Gorsuch ya samu kuri’u 60 kafin nadin na shi ya tabbata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.